Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Farashin Man Fetur Ya Fara Sassautowa A Bayan Da Yayi tashin gwauron Zabi A Sanadin Mahaukaciyar Guguwa Ta Katrina


Farashin man fetur da yayi tashin gwauron zabi a makon da ya shige ya sauko kadan jiya jumma’a, a bayan da Hukumar Kula da Mkamashi ta Duniya ta kara yawan man dake kasuwa daga rumbunan manta, omin maye gurbin wanda aka rasa a sanadin mahaukaciyar guguwa ta Katrina.

Mahaukaciyar guguwar ta janyo rufe rijiyoyin tonon mai ake cikin tekun Mexico, ta sa aka rufe matatun mai dake jihohin kudancin wannan kasa, abubuwan da suka haddasa karancin mai da karuwar farashinsa.

Wannan sanarwa ta jiya jumma’a ta yi tasiri nan take. A kasuwar hada-hadar haja ta New York, inda mahaukaciyar guguwar ta Katrina ta sa farashin danyen mai ya karu da kashi 2 da digo 6 cikin 100, sanarwar ta sanya farashin man da za a yi lodi cikin watan Oktoba ya fadi da kashi 2 da digo 3 cinkin 100 a cikin ’yan sa’o’i kadan.

Wannan hukumar kula da makamashi ta diya, wadda ta kunshi Amurka da wasu kasashe 25 masu sayen man fetur daga waje, wadanda ke da rumbunan adana mai domin ko ta kwana, zata kara ganga miliyan biyu na danyen mai kowace rana a kasuwannin mai na duniya.

Haka kuma kasashen zasu fito da tataccen mai idan suna da wanda suka adana a saboda rufe matatun mai da bututun tura su ya janyo karancinsa a nan Amurka.

Za a ci gaba da wannan aiki har na tsawon kwanaki akalla 30. Hukumar,mai hedkwata a birnin Pris ta ce nan da makonni biyu darektocinta zasu sake ganawa domin nazarin wannan lamari.

XS
SM
MD
LG