Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Idan Har Jama'a Zasu Fahimci Sana'ar Fim, Su Yi Mata Karbar Hannu Bibbiyu, To Allah Kadai ya san Irin Ci Gaban Da Za A Samu, In Ji Jaruma Zainab Abubakar


"Sana'ar fim ta kankama, kuma ta bazu sosai a fadin duniya."

Wannan kalamin, ya fito ne daga bakin jarumar fina-finan Hausa, Zainab Abubakar, wadda ta ce idan har Hausawa da masu kishin harshen Hausa zasu fahimci wannan sana'a, su gane cewar akwai fadakarwa tare da kariya a ciki, to lallai wannan sana'a zata buwaya ta dora kalmar Hausa a duniya.

A cikin hirar da ta yi da filin "A Bari Ya Huce..." jaruma Zainab Abubakar ta ce kowa da irin halinsa yake shiga. A saboda haka, kuskure ne babba a ce sana'ar fim ta 'yan iska ce, in ji jaruma Zainab Abubakar.

Zainab Abubakar, wadda iyayenta suka fito daga Yola da kuma Lagos, ta ce ai yadda su 'yan fim suke kama kai, da wuya a samu wata sana'ar da masu yinta suke mutunta kansu kamarsu, duk kuwa a saboda ganin cewa su na idanun duniya, komai suka yi zai yadu da sauri.

Idan ana son cikakkiyar hirar da Jaruma Zainab Abubakar ta yi da Ibrahim Alfa Ahmed, sai a matsa rubutun dake saman wanan labari inda aka rubuta "Saurari Hirar Zainab Abubakar."

XS
SM
MD
LG