Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Barnar Katrina


A yau ne ma’aikatan tsaro zasu daura damara, koda karfin tsiya, su fara kwashe sauran mutane masu taurin kan dake cewa su ba zasu bar garin New Orleans na nan Amurka ba, duk kuwa da hatsarin ci gaba da zama a birnin wanda ambaliyar ruwa tayi wa kaca-kaca bayan mahaukaciyar guguwar nan ta Katarina da ta abka masa. Tun jiya magajin garin birnin, Ray Nagin, ya bada umurnin a fara fitarda mutanen da karfin tsiya idan sun ki tafiya da kansu, bayanda aka fahimci cewa ci gaban zamansu a wurin barazana ce a gunsu ta kamuwa daga cututtukka daga gurbataccen ruwan da har yanzu ke cikin garin ko kuma gobarar dake tashi a wurare daban-daban. A yanzun ma injiniyoyi na ci gaba da aikin neman fitarda ruwan da ya kwararo a cikin garin na New Orleans bayanda wani shingen kare ruwan ya fashe. Mr. Nagin yace an riga an fitarda 60% na ruwan da ya mamaye 80% na birnin. Haka kuma yanzu an kebance wani wuri na musamman da zai zama gidan matattu, inda za’a rinkajibge tarin gawawwakin da ake tsamowa daga cikin ruwa da wasu wurare kamar gidaje. Koda yake hukuma na sa ran dubbai sun mutu, izuwa yanzu dai gawwawaki 71 aka riga aka gano. A jihar Mississippi ma an tsamo gawwawaki 150, amma can ma ana sa ran karshenta yawan matattun zai haya hakan.

XS
SM
MD
LG