Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ana Ci Gaba Da Kidaya Kuri'u A Kasar Iraqi


Har yanzu jami'an Iraqi su na ci gaba da kidaya kuri'un da aka jefa a kuri'ar-raba-gardama ta ranar asabar, inda sakamakon farko ya fara nuna alamun za a amince da daftarin tsarin mulki.

Jami'ai suka ce sakamakon farko ya nuna cewa an amince da kundin tsarin mulkin a wasu larduna guda biyu da 'yan mazhabin Sunni suke da rinjaye, Diyala da Nineva. Tun da fari an tsammaci za a ki yarda da tsarin mulkin a wadannan larduna. Za a yi watsi da wannan daftarin tsarin mulki idan har kashi biyu cikin uku na masu jefa kuri'a suka ki yarda da shi a larduna uku a kasar ta Iraqi.

Shugaba Bush ya yabawa 'yan Iraqi a saboda jefa kuri'ar da suka yi duk da barazanar kai hare-haren 'yan gwagwarmaya. Jami'ai suka ce fiye da kashi 60 daga cikin 100 na masu jefa kuri'a suka fito.

A halin da ake ciki, wani harin da sojojin Amurka suka kai ta sama ya kashe mutane 20 wadanda rundunar sojojin ta ce suna dasa bam ne a gefen hanya a kusa da Ramadi. Rundunar sojojin Amurka ta ce wasu hare-haren da sojojin taron dangi suka kai jiya lahadi a lardin al-Anbar sun hallaka 'yan tawaye 50. Amma kuma mazauna yankin sun ce akalla rabi daga cikin wadanda aka kashe fararen hula ne.

XS
SM
MD
LG