Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kulob Din Paris Ya Yafewa Nijeriya Kashi Sittin Na Basussukan Da Yake Binta


Gungun kasashe masu bayar da bashi wanda ake kira "Kulob Din Paris" ya cimma daidaituwa da Nijeriya kan yafewa kasar wani bangare na basussukan da yake binta.

Wannan yarjejeniya zata bai wa Nijeriya damar soke kimanin kashi sittin daga cikin 100 na bashin dala miliyan dubu 30 da wannan gungu yake binta.

Kulob din Paris mai wakilcin kasashe 19 ya ce yayi marhabin da wani gagarumin shirin tattalin arzikin da gwamnatin Nijeriya ta kaddamar a shekarar 2003, da kuma kwadayin da Nijeriya ta nuna na ficewa daga cikin wannan gungu na masu bayar da bashi.

Wannan shirin yafe bashi ya biyo bayan amincewar da Asusun Lamunin Kudi na Duniya, IMF, yayi cikin wannan makon da wani shirin da Nijeriya ta gabatar na gudanar da tattalin arzikinta. A cikin watan Yuni Kulob Din Paris ya ce ba zai fara tattauna sauke nauyin bashin dake kan Nijeriya ba sai bayan kasar ta kammala tattaunawar rage nauyin bashin da take yi da asusun IMF.

XS
SM
MD
LG