Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Dukkan Mutanen Dake Cikin Wani Jirgin Saman Fasinja Da Ya Fadi A Nijeriya Sun Mutu


Jami'an Kungiyar agaji ta Red Cross ta Nijeriya sun ce dukkan mutanen dake cikin wani jirgin saman fasinja kirar Boeing 737 sun mutu, a bayan da jirgin yayi hatsari a kan hanyarsa ta zuwa Abuja daga Lagos. Wannan hatsari ya faru jiya asabar da daddare, kuma an yi imanin cewa akwai mutane fiye da 115 cikin wannan jirgi.

Rahotanni na baya-bayan nan sun yi nuni da cewa babu wanda ya tsira da ransa, abinda ya saba da kalamun farko na wani jami'in Jihar da jirgin ya fadi a ciki wanda ya ce kimanin rabin mutanen dake ciki sun kubuta. Shi kansa wannan jami'i a yanzu ya ce babu wanda ya tsira da rai.

Jami'an kungiyar Red Cross sun fadawa kamfanonin dillancin labarai na kasa da kasa da suka tuntube su ta wayar tarho cewar babu alamar wani mai rai a inda jirgin ya fadi.

Gidan telebijin na AIT na Nijeriya ya nuna hotunan gawarwakin da suka kakkarye, suka kone, wasu ma gabobin jikin mutane ne kawai. Haka kuma ya nuna tikitin jirgin wani fasinja da garwar wani bbangaren jirgin. Gidan telebijin din ya ce an dauki wadannan hotuna ne a kusa da Lagos.

Hasumiyar dake kula da zirga-zirgar jirage a babban filin jirgin saman Murtala Muhammed na Lagos, ya kasa tuntubar wannan jirgi 'yan mintoci kadan a bayan da ya tashi zuwa Abuja da misalin karfe 8:45 na daren jiya asabar. An ce a lokacin akwai hadari na ruwan sama.

Wannan jirgi kirar Boeing 737 na kamfanin safarar jiragen saman Bellview Airlines ne, ewanda bai taba yin hatsari ba tun kafa shi shekaru 10 da suka shige a Nijeriya. Jirgin yana zirga-zirga a cikin Nijeriya da kuma wasu kasashe na Afirka ta Yamma, kuma yana da farin jini a wurin 'yan kasashen waje da kuma manyan jami'an gwamnati da 'yan kasuwa.

Kamfanin Bellview ba ya cikin jerin kamfanonin jiragen saman da hukumomin kula da lafiyar jiragen sama na kasa da kasa suke zargi da laifin rashin kulawa sosai da lafiyar jiragensu.

Rabon da a ga mummunan hatsarin jirgin sama a Nijeriya tun shekarar 2002 a lokacin da wani jirgin kamfanin EAS ya fadi kan gidajen jama'a a lokacin da yake kokarin tashi vdaga filin jirgin saman Aminu Kano, inda ya kashe mutane fiye da 140.

XS
SM
MD
LG