Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kotun Kolin Libya Zata Saurari Karar Ma'aikatan Jinya 'Yan Bulgariya Da Aka Daukaka Gabanta A Yau Lahadi


A yau lahadi kotun kolin kasar Libya zata saurari karar da aka daukaka ta wasu ma’aikatan jinya biyar ’yan kasar Bulgariya da wani likita Bafalasdine wadanda aka yi zargin sun sanyawa yaran kasar Libya kwayar cutar HIV mai haddasa kanjamau da gangan.

Ana jajiberen wannan shari’a, shugaban kasar Bulgariya, Georgi Parvanov, yace akwai hujja ta sa ran za a cimma wani abu a tattaunawar da ake yi ta neman sako ma’aikatan.

Wannan furuci na shugaban ya zo kwanaki kadan a bayan da jami’an Bulgariya da na Libya suka bayar da sanarwar cewa zasu kafa wani asusu na kasa da kasa da zai tallafawa yaran da suka kamu da cutar SIDA a Libya.

An yanke hukumcin kisa a kan ma’aikatan lafiyar su 6 a shekarar 2004 bisa tuhumar cewar da gangan sun sanya ma yara fiye da 400 kwayoyin cutar dake haddasa SIDA. Mutanen da aka kama a 1999 sun sha musanta wannan zargi. Kwararrun masana kiwon lafiya sun ce suna kyautata zaton rashin tsabta a wannan asibitin ne ya sa yaran suka kamu da cutar.

XS
SM
MD
LG