Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Wasu Mutane Sun Kashe Matar Alhaji Abubakar Rimi


'Yan sandan Nijeriya suna binciken mummunan kisan da aka yi wa matar wani sanannen dan siyasar Nijeriya mai adawa da gwamnatin Obasanjo, Alhaji Abubakar Rimi.

An tsinci gawar Sa'adatu Abubakar Rimi asabar a cikin falon dakinta, kuma a bisa dukkan alamu an yanka ta ne.

Wannan kisa ya biyo bayan karuwar tankiyar siyasa a wannan kasa mai arzikin man fetur.

Wata 'yar'uwar matar mai suna Halima ta fadawa kamfanin dillancin labari an Reuters cewa sun ji karar wani abu da karfi a jikin kofa, kuma da suka fito su binciki abinda ya faru sai suka ga Hajiya sa'adatu kwance jina-jina. Ta ce mutanen sun zo ne suka kashe ta kawai, ba su dauki komai a gidan ba.

Wakiliyar Muryar Amurka a Kano, Jamila Sulaiman Gezawa, ta ce an yi jana'izar marigayiyar da maraicen asabar a kofar gidan mai martaba Sarkin Kano, Alhaji Ado Bayero. Wadanda suka halarci jana'izar sun hada har da mataimakin shugaban Nijeriya, Alhaji Atiku Abubakar, da gwamnan Jihar Kano, Malam Ibrahim Shekarau da kuma wani tsohon gwamnan jihar kuma ministan tsaro, Rabi'u Musa Kwankwaso.

Tun da fari, wakilin Muryar Amurka a Kaduna, Ibrahim Garba, ya bayar da rahoton cewa jikin mutane yayi la'asar a wurin taron cikar shekaru arba'in da mutuwar Sardaunan sakkwato, Ahmadu Bello, a lokacin da labari ya iso zauren na kisan matar Abubakar Rimi. Alhaji Abubakar Rimi tare da gwamna Shekarau na Jihar Kano sun bar taron suka garzaya Kano.

An ce 'yan sanda sun kama masu gadin gidan, kuma sun kaddamar da bincike kan wannan lamarin da wasu mutane da dama suke dauka a zaman mai alaka da harkar siyasar Nijeriya.

Alhaji Abubakar Rimi tsohon gwamnan Jihar Kano ne, kuma ya kalubalanci shugaba Obasanjo a zaben fitar da dan takara na jam'iyyar PDP a zaben 2003. Kwanakin baya ya fice daga cikin jam'iyyar ta PDP, suka kaddamar da wata sabuwar jam'iyya mai suna "Movement for the Restoration of Democracy" domin su yi adawa da shirin da aka ce shugaba Obasanjo yana yi na neman wa'adi na uku kan karagar mulki.

XS
SM
MD
LG