Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shugaban Iran yaje Jaje a kasar Syria


Shugaban kasar Iran Mahmoud Ahmadi Nejad ya kai ziyara kasar Syria a wani mataki na kulla zumunci tsakanin kasashen yankin wadanda suke shan matsin lambar kasa da kasa da barazanar takunkumin karya tattalin arziki. Shugaban na kasar Iran ya sauka birnin Damaskas a yau Alhamis nan take ya kama hanya zuwa ofishin shugaban Syria Bashar Al-Asad inda suka fara tattaunawa. Mr. Ahmadi Nejad ya kai wannan ziyara ta kwanaki biyu Syria a daidai lokacin da kasashen su biyu suke funkantar matsin lamba daga kasashen Duniya. Amirka da kungiyar tarayyar kasashen Turai, suna son gabatar da kasar Iran gaban Kwamitin sulhu na MDD, domin ta matsa mata akan ta dakatar da ayyukan da takeyi na sarrafa makamashin Nukiliya. Itama kasar Syria tana fuskantar matsi da barazana daga kwamitin sulhu akan batun rikicin nan na kisan tsohon P. ministan Lebanon Rafik Hariri.

XS
SM
MD
LG