Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Mutanen Kauyukan Yankin Niger Delta Sun Fara Tserewa Daga Gidajensu


Mazauna kauyuka a yankin Niger Delta mai arzikin mai a kudancin Nijeriya su na arcewa daga gidajensu a yayin da gwamnati ta ke girka sojojinta a can.

Mazauna kauyukan su na fargabar fuskantar daukar fansa a bayan hare-haren da wasu mutanen da ake kyautata zaton ’yan dabar kabilar Ijaw ne suka kai a kan sojojin. An kashe sojoji fiye da 10 a hare-haren, abinda ya sa jita-jita ta fara bazuwa cewa hukumomi su na shirin kai wani gagarumin farmakin soja.

Jami’an kungiyoyin kare hakkin bil Adamsun ce sun damu da girka daruruwan sojojin da aka yi a kauyukan dake can cikin lungu.

An zargi sojoji da laifin kashe daruruwan mutane a kauyen Odi dake yankin na Niger Delta a 1999 domin daukar fansar kashe ’yan sanda su 12 da aka yi.

Ana kara girka sojoji a yankin a yayin da ’yan daba suke ci gaba da yin garkuwa da ma’aikatan mai hudu ’yan kasashen waje. An ce wadannan ’yan daba sun bukaci da a sako wasu shugabannin kabilar Ijaw biyu.

XS
SM
MD
LG