Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

'Yan Zanga-Zanga A Syria Sun Kona Ofisoshin Jakadancin Denmark Da Norway A Birnin Damascus


Dubban 'yan kasar Syria dake fusace, sun cinna wuta a ofisoshin jakadancin kasashen Denmark da Norway jiya asabar a Damascus, domin nuna rashin jin dadinsu dangane da zane-zanen batuncin da wasu jaridun kasashen suka buga na Annabi Muhammad mai tsira da aminci.

Wakiliyar Muryar Amurka a Damascus ta ce dubban mutane sun bayyana dauke da kwalaye masu rubutun yabon Ubangiji da addinin Musulunci.

An shirya cewar za a gudanar da zanga-zangar ce a cikin lumana. Amma ba a jima da farawa sai masu zanga-zanga suka fara jefa duwatsu kan ginin ofishin jakadancin Denmark. Sun samu keta shingayen da aka kakkafa suka cinna wuta a ginin.

Irin wannan lamari ya wakana a ginin ofishin jakadancin Norway, inda daga bisani 'yan sanda suka yi amfani da ruwa domin tarwatsa jama'a.

Har ila yau, 'yan sandan sun yi amfani da ruwa wajen tarwatsa daruruwan masu zanga-zanga da suka taru a kofar ofishin jakadancin Faransa, aka kuma girka 'yan sandan kwantar da tarzoma a kofar ofishin huldar Amurka.

Wannan ita ce zanga-zanga mafi muni da aka yi ya zuwa yanzu dangane da buga wasu zane-zanen Annabi Muhammad Sallalahu Alaihi wasallam, inda a zane guda daya aka nuna shi sanye da rawani da aka yi masa siffa kamar bam.

Kasashen Norway da Denmark sun bukaci dukkan 'yan kasashensu da su bar Syria.

Wata jaridar kasar Denmark ita ta fara buga wadannan zane-zane a watan Satumbar bara, wasu jaridun kasashen turawa kuma suka sake buga su daga baya.

A halin da ake ciki, shugaba Mahmoud Ahmadinejad na Iran ya umurci jami'an kasar da su nazarci soke dukkan ayyukan kwangila da kasashen da jaridunsu suka buga wadannan zane-zanen.

Ita ma fadar Paparoma ta Vatican ta yi Allah wadarai da buga zane-zanen na batunci ga Annabi Muhammad, Sallallahu alaihi Wasallam, tana mai fadin cewa 'yancin fadin albarkacin baki ba wai yana nufin 'yancin cin mutuncin addinin wani ba ne.

"'Yancin tunani da na bayyana ra'ayi, wanda aka tabbatar a cikin Kundin hakkokin Bil Adama, ba zai 5taba hadawa da ikon cin mutunci ko bakanta imanin wasu mutane ba, kowane irin addini suke bi kuwa" in ji fadar ta Vatican cikin wata sanarwar da ta bayar asabar din nan.

XS
SM
MD
LG