Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kamfanin Mai Na Shell Yace Mahara Sun Lalata Wani Bututun Mansa Ranar Jumma'a A Nijeriya


Kamfanin mai na Shell ya ce wasu mahara sun lalata wani bututu ranar jumma'a a Nijeriya, amma kuam harin bai shafi yawan man da take hakowa ba.

Kamfanin na Shell ya fada litinin din nan cewa harin ya lalata wasu mahadar bututun mai guda biyu a kan wani layin bututu kusa da kauyukan Agge da Agoro a kudu maso gabas da Lagos.

Kamfanin ya ce an saba yin amfani da wannan bututu wajen tura danyen mai zuwa tashar lodin mai zuwa kasashen waje ta Forcados, amma kwanakin baya aka daina tura mai ta wannan bututu a saboda fargabar tsaro.

A ranar lahadi, wata kungiyar 'yan daba ta yi barazanar kai sabbin hare-hare a kan cibiyoyin mai dake yankin Niger Delta mai fama da fitina.

'Yan dabar su na bukatar bai wa yankin karin ikon mallakin arzikin mai na yankin tare da sako wasu shugabannin kabilar Ijaw guda biyu dake daure.

Hare-hare a yankin ya sa yawan man da Nijeriya take hakowa ya ragu da kimanin kashi 20 daga cikin 100 a kwanakin nan daga ganga miliyan biyu da rabi da ta saba hakowa kullum.

XS
SM
MD
LG