Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kwamitin Ibrahim Mantu Ya Amince Da Karawa Shugaban Kasa Yawan Wa'adin Da Zai Iya Yi Kan Mulki A Nijeriya


Wani Kwamitin hadin guiwa na majalisun dokokin tarayya biyu a Nijeriya ya ce ya kamata a kyale shugaban kasa yayi wa'adi uku a kan karagar mulki, daga ka'idar wa'adi biyun dake cikin tsarin mulkin yanzu.

Idan har majalisun dokokin tarayya suka amince da wannan shawara, to an share ma shugaba Olusegun Obasanjo hanyar sake neman kujerar shugabanci ke nan idan wa'adinsa na biyu ya cika a shekara mai zuwa.

'Yan majalisar dattijan dake sake nazarin tsarin mulkin a karkashin jagorancin mataimakin shugaban majalisar, Ibrahim Mantu, sune suka bayar da wannan shawara a karshen zaman da suka yi da maraicen alhamis a birnin Fatakwal.

Koda yake kwamitin bai bayyana cewa ko wa'adi uku kan kujerar mulkin zai faro ne daga shugaba mai ci ba, kusan kowa a Nijeriya yayi imani da cewa shugaba Olusegun Obasanjo yana kokarin yayi "Tazarce" ne.

'Yan majalisar dake yin adawa da wannan kokari na Tazarce sun fice daga zauren taron na Fatakwal, inda wasunsu suka ce ofishin shugaba Obasanjo ne ya kitsa dukkan abubuwan da suka faru a wurin zaman.

Wani dan majalisar yayi kashedin cewa za a samu karin tankiya a cikin Nijeriya, kuma yin hakan zai iya barin shugaban da ba ya tabuka komai ya shafe shekaru 12 yana kan kujerar jagorancin kasar.

A lokacin da yake bayyana wannan "shawara" ta su, mukaddashin shugaban majalisar dattijai, Ibrahim Mantu, ya ce kwamitinsa na sake nazarin tsarin mulkin, yana so ne, "ya daidaita tsarin mulkin da ra'ayoyin al'ummar Nijeriya" a cewarsa.

XS
SM
MD
LG