Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Gwamnatin Nijar ta soki kafofin yada labaran yammaci da laifin...


Gwamnatin jamhuriyar Niger ta cacaki kafofin yada labarun kasa da kasa a saboda bada rahotanin cewa akwai shedar matsalar karacin abinci a kasar. Mai magana da yawun gwamnatin Niger Ben Umar ya fadawa sashen Hausa na Muryar Amirka cewa ’yan jarida a Niger suna ci gaba da bada rahotanin kage akan matsalar abinci a kasar a saboda haka yace ba za’a kara baiwa ’yan jaridar ’yancin cin karensu babu babaka wajen bada rahotanin akan wannan batu ba.

A farkon wannan makon gwamnatin Niger ta fadawa yan jaridar BBC cewa an soke izinin su ta bada rahotani akan wannan batu, bayan da suka bada rahotanin cewa akwai shedar karancin abinci a ƙasar. Mr Omar yace gwamnati tana da hujjar daukan wannan mataki. Yace yanzu Niger bata fuskantar matsalar karancin abinci sai da matsalar tattalin arziki. Haka kuma ya zargi kafofin yada labaru da laifin bada rahotanin karya akan wannan al’amari a bara.

A cikin shekara ta dubu biyu da biyar kungiyoyin agaji sun fada cewa kimamin mutane miliyan uku ke fuskantar matsalar karancin abinci a jamhuriyar Niger.

XS
SM
MD
LG