Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Gwamnatin Chadi Ta Ce Sojojinta Sun Kwato Wani Garin Da 'Yan Tawaye Suka Ce Sun Kama


Jami'an gwamnati a kasar Chadi sun ce dakarunsu sun sake kwato wani muhimmin garin da 'yan tawaye suka ce sun kama ranar talata.

Har yanzu babu tabbas game da halin da ake ciki a zahiri a garin Mongo dake tsakiyar kasar, yayin da shugabannin 'yan tawaye suke fadawa kamfanonin dillancin labarai cewar har yanzu akwai wasu sojojinsu a cikin garin. Ministan tsaro na Chadi, Issa Djadallah, ya ce dakarun gwamnati sun yi amfani da jiragen saman helkwafta domin fatattakar 'yan tawayen.

Kungiyar 'yan tawaye mai suna Hadaddiyar Kungiyar Kawo Sauyi, tana kokarin hambarar da shugaba Idris Debu daga kan mulki. Wannan farmaki a kan garin Mongo shine karon farko da 'yan tawaye suka kusanci N'Djamena, babban birnin kasar, da tazarar kilomita 400.

A ranar litinin, 'yan tawaye sun kai farmaki a kan sansanin 'yan gudun hijira na Goz Amer dake gabashin Chadi, inda suka kashe jami'an tsaron gwamnati da dama.

Kungiyar 'yan tawayen ta hada da tsoffin sojojin gwamnati da suka canja sheka.

Hukumar Kula da 'Yan Gudun Hijira ta Majalisar Dinkin Duniya, wadda ke gudanar da sansanonin 'yan gudun hijirar Sudan a gabashin Chadi, ta ce zata fara kwashe ma'aikatanta daga yankin.

XS
SM
MD
LG