Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shugaba Idris Deby Na Chadi Ya Ce Kasarsa Zata Tsinke Hulda Da Sudan...


Shugaban kasar Chadi, Idris Deby, ya ce kasarsa za ta tsinke huldar jakadanci da Sudan, wadda ya zarga da laifin goyon bayan 'yan tawayen ad suka kai farmaki a babban birnin Chadi jiya alhamis.

Shugaba Deby yayi magana wajen wani gangami yau jumma'a, kwana guda a bayan dauki-ba-dadin da aka yi a birnin N'Djamena, har aka kashe mutane dari uku da hamsin in ji ministan kula da yankunan kasa, Mahamat Ali Abdullahi Nassour.

Shugaba Deby yayi barazanar korar 'yan gudun hijira na Sudan su dubu maitan dake zaunea a Chadi, sai fa idan kasashen duniya sun dauki matakan kawo karshen abinda ya kira kokarin Sudan na gurgunta gwamnatinsa.

Sudan ta sha musanta cewar tana goyon bayan kungiyar 'yan tawayen wadda ta kunshi tsoffin sojojin gwamnatin Chadi da dama.

A yau jumma'a, a wani adndali dake birnin N'Djamena, gwamnatin Chadi ta yi faretin mutanen da aka kama a lokacin fada na jiya. Jami'ai suka ce mutane maitan ne suka ji rauni a lokacin gumurzun na jiya alhamis.

A jiya alhamisar, shugaba Idris Deby ya ayyana samun nasara a kan 'yan tawaye, wadanda suka kai farmaki kan babban birnin kasar bayan da suka yi mako guda su na kai hare-hare a wasu yankuna na kasar Chadin.

XS
SM
MD
LG