Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shugaba Idris Deby Na Chadi Ya Musanta Cewar Yana Fakewa Da Zargin Sudan Domin Boye Matsalolin Kasarsa


Shugaba Idris Deby na kasar Chadi yayi kira ga kasashen duniya da su kara taka rawa wajen warware tashin hankalin da ake ci gaba da fama da shi a yankin Darfur na Sudan, su kuma kara karfin tsaron lafiyar ’yan gudun hijira dubu maitan na Sudan da suke zaune a cikin hamadar gabashin Chadi.

Wani wakilin Muryar Amurka a N'Djamena, ya ce daga lokacin da ’yan tawaye suka kai farmaki a kan N’Djamena, babban birnin Chadi, a makon jiya, shugaba Idris Deby ya sha fitowa yana dora wa kasar Sudan laifin goyon bayan wadannan ’yan tawaye. A cikin hirar da yayi da gidan rediyon Muryar Amurka, shugaba Deby ya ki yarda ya kira maharan da sunan ’yan tawaye. A lokacin da yake wannan hira daga hedkwatar jam’iyyarsa, shugaban na Chadi ya ce sojojin haya ne. Ya ce Sudan ce ta biya su, ta horas da su ta kuma ba su umurnin su kai hari Chadi.

A yayin da shugaba Deby yake ci gaba da kokarin dora laifin wannan fitina a kan kasar Sudan, mutane da yawa a babban birnin sun ce wannan rikici da ake yi a cikin Chadi yana da asali daga irin matsalolin cikin gida da kasar take fuskanta. A bangare guda ma, dukkan jam’iyyun hamayya na Chadi suna kauracewa zaben shugaban kasar da ake shirin gudanarwa ranar 3 ga watan Mayu.

Shugaba Deby ya mayar da martani ga masu sukar lamirin dake cewa yana yin amfani da irin rawar da ake zargin Sudan da takawa domin yin rufa-rufar irin munanan matsalolin cikin gida dake addabar Chadi, ciki har da fitina dake karuwa a saboda talaucin da yayi kanta, da rashin dimokuradiyya, da kuma zargin cewa gwamnatinsa tana yin rub da ciki a kan arzikin man fetur na Chadi. Ya ce, "...ta yaya zan yi amfani da wannan mummunar rana da sojojin haya na Sudan suka kawo hari a kan babban birninmu domin cimma wani guri na. Ta yaya zan yi amfani da wannan domin boye matsalolin cikin gida?"

Shugaba Deby dai ya kauce daga barazanar da yayi ta korar ’yan gudun hijirar Sudan, amma kuma ya ce a yanzu ba zai iya tabbatar da tsaron lafiyarsu ba. Ya ce ba ya da sojojin da zai iya fatattakar duk wani farmakin da sojojin haya na Sudan zasu kawo, tare da samar da tsaro ga ’yan gudun hijira dubu 200 na Sudan a lokaci guda. Shugaba Deby yana son kasashen duniya, musamman Amurka, su kara taka rawa wajen warware rikicin Darfur, wanda a bayan shafar Chadi, yana shafar kasar Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya.

Ya ce, "A cikin watannin Fabrairu da Afrilu na rubuta wasika da hannu na zuwa ga shugaba Bush, kuma a yanzu ma sako na iri daya ne: ya kamata babbar kasar mafi tasiri a duniya ta sa hannu."

Shugaba Omar Hassan al-Bashir na Sudan ya ce kasarsa ba ta da wata sha’awa ta ganin rashin kwanciyar hankali a Chadi makwabciyarta. Amma masu fashin baki da dama a yankin suna ganin cewa Sudan tana taka rawa a rikicin na Chadi.Sun yi nuni da cewa shi kansa shugaba Idris Deby ya zamo shugaba ne a wani juyin mulkin 1990 a lokacin da yake jagorancin sojojin ’yan tawayen da Sudan take marawa baya.

XS
SM
MD
LG