Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Hare haren Bamabamai sunyi sanadiyyar mutuwar 'yan Iraq da dama


Wani labari mai dumi yace Jerin wasu hare-haren da aka kai da motoci cike da bama-bamai sun halaka ’yan kasar Iraq a kalla 14, wasu kuma, fiye da tamanin sun jikkata. Motoci bakwai cike da bama-bamai ne su ka jijjiga birnin Baghadaza a jiya litinin, kuma su ka yi sanadiyar mutuwar mutane takwas a kalla. Bama-baman sun tashi ne a wajejen ma’aikatar kiwon lafiya, da wata jami’a da kuma sauran sassan birnin.

Wasu ’yan kasar Iraki shidda kuma, harbe su aka yi da bindigogi har lahira. A wani al’amari na daban kuma, hukumomi sun ce an gano gawawarkin mutane 17 a kalla a birnin Baghadaza. Haka kuma a jiya litinin din, an ci gaba da yin shara’a ga Saddam Hussein da abbokan laifin shi bakwai, amma na dan wani gajeren lokaci. Kotun ta saurari wani kaset, mai dauke da muryoyin Saddam da mukarrabansa da ake zargi da laifi, ga dukan alamu su na tattaunawa game da shirin nuna halin ba sani ba sabo ga ’yan Shi’a a kauyen Dujjail a shekarar 1982. Kotun ta dage zaman shari’ar, har sai ranar 15 ga watan gobe na mayu. Wadannan abubuwa na faruwa ne a daidai lokacin da firayiminsta mai jiran gado Jawad-al-Maliki ya ke kokarin kafa wata gwamnatin hada kan kasar ta Iraki.

XS
SM
MD
LG