Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Babban Lauyan Dake Gabatar Da Kararraki A Kotu Ta Musamman Ta Saliyo Ya Ce Zai Sauka Idan Kwantarakinsa Ya Kare A Karshen Watan Yuni


Babban lauyan dake gabatar da kararraki a gaban Kotu ta Musamman (mai bin kadin laifuffukan yaki) a Saliyo, Desmond de Silva, ya ce zai sauka daga kan wannan mukami idan kwantarakinsa ya kare a karshen watan Yuni.

A cikin sanarwar da ya bayar, de Silva ya ce a lokacin da aka nada shi babban mai gabatar da kararraki a kotun a 2005, yayi alkawarin yin bakin kokarinsa domin gurfanar da tsohon shugaban Liberiya, Charles Taylor, a gaban wannan kotu.

Ya ce ya cika wannan alkawari. Ya kuma yi nuni da cewa zai iya yarda ya komo ya shugabanci wannan shari'a a duk lokacin da aka fara gudanar da ita.

Kotun ta Saliyo mai samun tallafin Majalisar Dinkin Duniya tana rike da Taylor, amma kuma a bisa dalilai na tsaro, kasar ta bukaci da a dage shari'ar zuwa kasar Netherlands inda kotun duniya take.

Kasar Netherlands ta ce zata yarda ta karbi bakuncin wannan shari'a, amma kuma bisa sharadin cewa Taylor zai bar kasar a bayan wannan shari'a ko an same shi da laifi ko a'a.

Wasu kasashen Turai uku da aka tuntuba sun ki yarda su karbi tsohon shugaban na Liberiya a bayan shari'arsa. kasashen su ne Austria da Sweden da kuma Denmark.

Ana tuhumar Mr. taylor da laifin goyon bayan 'yan tawaye na Saliyo a lokacin kazamin yakin basasar kasar.

XS
SM
MD
LG