Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shugaba Idris Deby Ya Gudanar Da Yakin Neman Zabensa Na Karshe A N'Djamena


Shugaba Idris Deby na Chadi ya gudanar da yakin neman zabensa na karshe kafin zaben shugaban kasar da za a gudanar jibi laraba. Sai dai kuma, ana tababar ko za a iya gudanar da wannan zabe tsakani da Allah a bayan da ’yan adawa suka ce zasu kauracewa zaben, yayin da shi kuma shugaba Deby ya ki yarda a jinkirta gudanar da zabe a bayan harin da ’yan tawaye suka kai babban birnin kasar.

Dubban 'yan kasar ta Chadi sun cike babban filin wasa na kasa jiya lahadi domin kallon wannan kyamfe, a yayin da daruruwan 'yan sandan kwantar da tarzoma da sojoji suke gadi.

A cikin jawabinsa, Mr. Deby ya sake nanata zargin cewa gwamnatin Sudan ce ta kitsa harin da 'yan tawaye suka kai kan birnin N'Djamena a watan da ya shige. Sudan dai ta musanta cewar tana goyon baya ko tallafawa 'yan tawayen.

Wannan fada a babban birnin ya sa jami'an diflomasiyya daga kasashen Afirka da Turai da kuma Amurka sun roki Chadi da ta jinkirta zaben. Gamayyar manyan jam'iyyun adawa ta ce zata kauracewa zaben a saboda ba za a gudanar da shi tsakani da Allah ba.

Haka kuma, shugaban kungiyar kare hakkin bil Adama ta kasar Chadi ya ce kyale Mr. Deby yayi Tazarce zai haddasa kara tauye hakkokin al’ummar Chadi.

XS
SM
MD
LG