Babban jami'in ayyukan jinkia na Majalisar Dinkin Duniya ya tsere daga wani sansanin mutanen da suka rasa matsuguni a yankin Darfur mai fama da fitina, a bayan da 'yan zanga-zanga suka rikide suka koma masu tayar da fitina a sanadin wani sabani.
Ala tilas Jan Egeland da 'yan tawagarsa suka arce daga sansanin Kalma litinin din nan a lokacin da gungun masu zanga-zangar dake neman karin kariya daga sojojin kiyaye zaman lafiya na MDD, suka kai farmaki a kan wani tafinta. An yada jita-jitar cewa shi wannan tafinta yana da alaka da kungiyar banga ta Janjaweed wadda aka dora wa alhakin akasarin tabargazar da aka aikata a yankin Darfur.
Egeland da ma'aikatan agaji sun koma Nyala, babban birnin lardin Darfur ta kudu. Daga baya, ya fadawa 'yan jarida cewar a bayan da tawagarsa ta bar sansanin, gungun jama'a sun kai farmaki a kan tashar 'yan sandan Kungiyar Tarayyar Afirka suka kashe wani tafinta.
Wannan ziyara ta Egeland ta biyo bayan yarjejeniyar zaman lafiyar da aka kulla a tsakanin babbar kungiyar 'yan tawaye ta Darfur da gwamnatin Sudan. Wasu kungiyoyin 'yan tawayen biyu ba su yarda da wannan yarjejeniya ba.