Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Rundunar Sojojin Sudan Ta Musanta Ikirarin 'Yan Tawaye Cewar Ta Kai Farmaki Kan Wani Sansaninsu


Rundunar sojojin Sudan ta musanta ikirarin da 'yan tawaye suka yi cewar sojojin gwamnati sun kai farmaki a kan wani sansanin 'yan tawaye, abinda ya keta yarjejeniyar zaman lafiya ta Darfur da aka kulla.

A yau litinin shugabannin kungiyar 'yan tawaye ta "SLA" suka ce sojojin gwamnati tare da sojojin sa kai masu goyon bayansu suka kai hari a kan sansanin 'yan tawayen dake Dar-es-Salam, a yankin Darfur ta Arewa.

Babu cikakken bayanin lamarin. Amma kuma masu magana da yawun sojojin Sudan sun ce babu gaskiya a cikin zarge-zargen cewa sojojin gwamnati sun kai farmaki.

Kungiyar 'yan tawaye mafi girma a yankin Darfur ta sanya hannu a kan yarjejeniyar zaman lafiya tare da gwamnati a ranar 5 ga watan nan na Mayu domin kawo karshen fadan shekaru uku da watanni a yankin. Wasu kananan kungiyoyin 'yan tawaye biyu sun ki yarda su sanya hannu a kan yarjejeniyar.

A halin da ake ciki, wasu wakilan Majalisar Dinkin Duniya zasu isa Khartoum ranar talata domin tattaunawa da gwamnati dangane da shirin da ake yi na girka sojojin kiyaye zaman lafiya na majalisar a Darfur.

Har yanzu Sudan ba ta amince da wannan aiki na MDD ba, tana mai fadin cewa tana son karin bayani game da girma da kuma tsarin aikin wannan runduna tukuna.

XS
SM
MD
LG