Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Buzaye 'Yan Tawaye Sun Kwace Sansanonin Sojan Gwamnati Biyu A Arewa Maso Gabashin Mali


Jami’an soja a kasar Mali sun ce wasu mutanen da ake kyautata zaton Buzaye ’yan tawaye ne, sun kwace wasu sansanonin soja guda biyu a yankin arewa maso gabashin kasar.

An kai wadannan hare-hare tun da sanyin safiyar yau talata a kusa da garin Kidal. Shaidu sun ce sun ji kararrakin bindigogi, amma ba a samu rahoton jikkata ba.

Har ila yau an samu wani rahoton da ba a tabbatar da shi ba wanda ke cewa daga baya ’yan tawayen sun mamaye garin, suka kwace wasu gidajen rediyo guda biyu.

Al’ummar Buzaye dai makiyaya ne wadanda suka yi shekaru aru aru suna kai-komo a yankunan hamada na arewacin Mali. A cikin shekarun 1990, ’yan tawaye sun zargi gwamnatin tarayya da yin watsi da su, suka kuma tayar da kayar baya.

Yarjejeniyar zaman lafiyar da aka kulla ta kawo karshen bai wa hammata iska, an kuma dauki wasu daga cikin ’yan tawayen aiki a rundunar sojojin kasar Mali. Amma kuma an ci gaba da samun fada jefi jefi.

XS
SM
MD
LG