Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Amnesty International Ta Zargi Amurka Da Manyan Kasashen Duniya Da Laifin Take Hakkokin Bil Adama


Kungiyar "Amnesty International" ta zargi Amurka da wasu manyan kasashen duniya dake da hannu a yaki da ta'addanci da laifin take hakkokin bil Adama.

A cikin rahotonta na shekara-shekara, kungiyar ta kare hakkin bil Adama mai cibiya a London, ta soki abinda ta kira "yaudara da alkawuran karya" na gwamnatocin manyan kasashe, ciki har da ta Amurka, da Britaniya da sauran kasashen Turai, da Rasha da kuma kasar Sin.

Musamman ma, babbar sakatariyar kungiyar, Irene Khan, ta ware Amurka cikin wadanda ta fi suka a saboda tsare mutanen da ta ke zaton 'yan ta'adda ne na lokaci mai tsawo a sansanin Guantanamo dake tsibirin Cuba.

Har ila yau Ms. Khan ta bayyana damuwa ta musamman da rikicin da ake yi a yankin Darfur na Sudan, inda ta soki kasashen Sin da Rasha da kakkausar harshe a saboda himmar da suka sanya ta kare muradun tattalin arzikinsu a Sudan.

Rahoton ya koka da cewa an sanya kafa an take manufofi na alheri a wajen yaki da ta'addanci, yayin da shugabannin kasashe da yawa suka kawar da idanunsu daga dimbin matakan keta hakkin bil Adama a darfur da Chechnya da wasu wuraren da ake rikici.

Har ila yau, kungiyar Amnesty ta ce hakkokin bil Adama su na fuskantar barazana a kasashen Colombia, da Afghanistan da Iran da Uzbekistan da kuma Koriya ta Arewa.

XS
SM
MD
LG