Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Hukumomin Islama A Somaliya Sun Ce Sun Kwace Babban Birnin Kasar Daga Hannun Mayakan Sojojin Sa Kai


Hukumomin Islama a Somaliya sun ce sun ce sun kwace babban birnin kasar a bayan fadan makonni a tsakaninsu da mayakan wasu kungiyoyin sojan sa kai.

Shugaban Kotunan Islama a Mogadishu, Sheikh Sharif Sheikh Ahmed, ya bayyana samun nasara kan kawancen sojojin sa kan a lokacin wani jawabin da ya gabatar a rediyo litinin. Ya roki mazauna birnin da su yi na'am da sabbin shugabanninsu, yana mai fadin cewa kotunan su na kwadayin maido da zaman lafiya da tsaro a birnin.

Mayakan Islama masu alaka da kotunan Shari'a sun fatattaki mayakan sa kai daga wurare da dama da suka yi tunga a Mogadishu a cikin mako gudan da ya shige. Sun samu wata babbar nasarar ranar lahadi a lokacin da suka kwace garin Balad, suka tsinke hanyar samun kayan fada na kawancen sojojin sa kai.

An ce akasarin shugabannin kungiyoyin sojan sa kai na Mogadishu sun tsere daga birnin. Mazauna birnin suka ce mayakan kungiyoyin sun fara mika makamansu ga sojojin Islama.

An kashe mutane 350 a fadan da aka gwabza har sau uku a tsakanin bangarorin biyu tun daga watan Fabrairu.

XS
SM
MD
LG