Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ana Tuhumar Wasu Mutane Bakwai Da Kulla Makarkashiyar Kai Hare-Haren Ta'addanci A Cikin Amurka


Atoni janar na Amurka, Alberto Gonzalez, ya ce an tuhumi wasu mazaje bakwai daga birnin Miami bisa zargin kokarin hada baki da kungiyar al-Qa’ida domin kai munanan hare-hare a cikin Amurka.

Gonzalez ya fada yau jumma’a a nan Washington cewa mutanen sun so su dasa bam a gini mafi tsawo a nan Amurka, watau ginin nan da ake kira "Sears Tower" a birnin Chicago, da kuma wasu gine-ginen gwamnati a ciki da wajen birnin Miami. Amma kuma ya ce kulle-kullensu ba su wuce shirya yadda zasu iya kai hare-haren ba.

Har ila yau ya ce ba su taba yin hulda da kungiyar al-Qa’ida ba, sai dai da wani mutumin da yayi shiga ya ce musu shi dan kungiyar ne.

Atoni janar din ya ce mutanen sun so su kaddamar da hare-haren da suka kai, ko suka zarce, munin hare-haren 11 ga watan Satumbar 2001. Ya bayyana mutanen a zaman ’yan ta’adda goyon cikin gida.

Ya ce biyar daga cikinsu Amurkawa ne, daya mai takardar iznin zama a wannan kasa, dayan kuma dan kasar Haiti dake zaune ba tare da izni ba a cikin wannan kasar.

Darektan hukumar binciken manyan laifuffuka ta tarayya a nan Amurka, FBI, Robert Mueller, ya fadawa ’yan jarida lokacin wani tari a Cleveland a jihar Ohio cewa shugaban wannan gungu ba Amurke ne.

XS
SM
MD
LG