Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Firayi ministan Palasdinawa ismail Haniyeh na kungiyar hamas ya bukaci Isra’ila akan ta daina kai hare hare a yankin zirin Gaza


Firayi ministan Palasdinawa ismail Haniyeh na kungiyar hamas ya bukaci Isra’ila akan ta daina kai hare hare a yankin zirin Gaza, duk da haka ya ce yana aiki tukuru na warware wannan rikicin dake tsakaninsu game da sace wani sojin isra’ila da akayi.

Mr. Haniyeh ya yi wannan jawabi bayan sallar Jumma’a a Gaza cewa hare haren da Isra’ila ke kaiwa da niyar kwato wannan soja yana dada bata al’amarin. Mayakan sa kai na Palasdinawa sun sace wani sojan Isra’ila a lokacin da suka kai wani sumame a wani ofishin sojan a ranar lahadi.

Sojojin Isra’ila suna ci gaba da kai hare hare da jiragen sama da kuma bindigogin igwa, abinda ya hana sojojin kasa shiga yankin a domin matsawa ta fuskar siyasa.

A birnin Gaza, kafofin Palasedinawa sun ce wani harin ta jiragen sama da isra Ila ta kai a kan wata mota, ta jiwa akallan wani mayakin sa kai guda rauni.

A wani gefen kuma rundunar sojan Isra’ila ta fada ayau cewa, ta kashe ‘yan bindiga biyu a wani hari da ta kai a yammacin kogin Jordan a garin Nablus.

A wani labari makamancin wannan, wani dan kungiyar al-Aqsa Brigade ya fada a yau cewa kungiyar ta kame wani sojan Isra’ila daya to amma kamfanin dillancin labarum Ruwaitas ya ce shugaban kungiyar ya janye wannan kalami da suka yi.

XS
SM
MD
LG