Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Babban sakataren MDD Kofi Annan ya bayyana imanin cewa komai ta dade, watan wata rana za’a ga sojan kiyaye sulhun MDD din sun shiga yankin Darfur


Babban sakataren MDD Kofi Annan ya bayyana imanin cewa komai ta dade, watan wata rana za’a ga sojan kiyaye sulhun MDD din sun shiga yankin Darfur na yammacin Sudan don kashe wutar rikicin dake cin yankin. Mr. Annan yana wannan kalamin ne yayin haduwarsa da shugaban Sudan Omar al-Bashir a birnin Banjul na kasar Gambia inda aka kamalla taron kolin shugabannin kasashen Afrika, wadanda kuma suka dauki lokaci suna duba matsalolin tashin hankalin dake addabar Somalia da Darfur din.

Mr. Annan yace shi da shugaba al-Bashir sun ajiye cewa zasu ci gaba da zantawa kan wannan maganar neman tura sojan MDD din zuwa Darfur, amma tun jiya Lahadi ma aka sa ran cewa shugabannin kasashen na Afrika zasu kara kaimi ga matsin lambar da suke wa Sudan na ta bar wadannan sojan na MDD suje Darfur, su maye gurjbin rundunar sojan kasashen Afrika dake niyyar janyewa a watan Satumban wannan shekara. Ita ma Somalia, shugabannin Afrika din na tunanin su aika mata nasu sojoji a cikinta. A wurin taron ne kuma shugaban kasar Senegal, Abdoulaye Wade ya bada sanarwar niyyar gwamnatinsa na gurfanarda tsohon shugaban Chad Hissene Habre a gaban kotu don a chaje shi da laifukkan yaki. Tsohon shugaban na Chad dai yana zaune ne a Senegal tun bayanda aka tumbuke gwamnatinsa a 1990.

XS
SM
MD
LG