Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Yau Amurka Ta Ke Cika Shekaru 230 Da Samun 'Yanci


A yau talata ne Amurkawa suke bukukuwan cikar shekaru dari biyu da talatin da kwatar 'yancin kasarsu.

Bukukuwan 'yanci na ranar 4 ga watan Yuli, su na karrama ranar da a cikin shekarar 1776 majalisar dokokin nahiya dake wakiltar yankuna (jihohi) goma sha uku na asali na wannan kasa da ake kira Amurka a yanzu, ta ayyana 'yancin yankunan daga mulkin Ingila.

A cikin garuruwa da biranen dake fadin wannan kasa, Amurkawa za su gudanar ad bukukuwa ko liyafa ko fareti ko halartar wasannin mawaka tare da kallon wasan wuta da zarar rana ta fadi.

A Washington, babban birnin tarayya, za a fara bukukuwa tare da yin wani fareti na 'yan badujala, da 'yan rawa da kuma kungiyoyin al'umma dabam-dabam.

da maraicen yau talata, za a gudanar da wasannin mawaka a kofar ginin majalisar dokoki dake dab da ginin Muryar Amurka, daga baya kuma za a gudanar da daya daga cikin wasannin wuta mafi girma a fadin wannan kasa.

XS
SM
MD
LG