Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Sakatariyar harkokin wajen Amirka ta je birnin Beirut


Sakatariyar harkokin wajen Amirka Condelizza Rice ta kai wata ziyarar ba-zata birnin Beirut domin tattaunawa da firayiministan kasarLebanon Faouad Sinora game da hare haren da isra’ila ta ke kaiwa kan Hezbullah a Lebanon. Sakatariya Rice ta godewa shugaban kasar Lebanon din bisa irin juriya da karfin halinsa a daf da lokacin da suka fara tattaunawarsu.

Kafin ta tashi zuwa kasar Lebanon sai da ta shiga wani jirgin saman mai saukar angulu cike da jami’an tsaro daga Cyprus domin fara wannan ziyara ta yankin gabas ta tsakiya. Ana sa rai zata maida hankali wajen samo tallafi ga fararen hular kasar Lebanon. Daga birnin Beirut ne ake sarai Mrs Rice za ta wuce birnin kudus domin tattaunawa da fiyayiminstan Isra’ila, Ehud Olmert daga nan ta je yammacin kogin Jordan domin tattaunawa da shugaban Palasdinawa Mahmoud Abbas.

A birnin London firayiministan Birtaniya Tony Blair ya nayyana halin da ake ciki a kasar Lebanon da cewa abin takaici ne. kan ya ce yana fatar nan da kwanaki kadani masu zuwa za’a bada sanarwa a game da wani shiri na tsaida wannan yakin. Akan hanyarta ta zuwa kasar Lebanon sakatariyar harkokin wajen Amirka ta ce tana aiki a kan wani mataki na hanzari da zai kawo shirin tsagaita bude wuta a wannan fada ta yanzu yakai ranarsa ta goma sha uku.

Duk da haka ta ce duk wani matakin tsagaita bude wuta dole ne ya hada da musabbabin wannan tashin hankali, watau barazanar da kungiyar Hezbullah ke yiwa Isra’ila.

XS
SM
MD
LG