Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Kashe Sojojin Majalisar Dinkin Duniya A Wani harin Da Isra'ila Ta Kai Kan Tasharsu A Lebanon


Majalisar Dinkin Duniya, MDD, ta ce an kashe sojojin kiyaye zaman lafiyarta hudu a wani harin da Isra'ila ta kai daga sama a kan tasharsu dake kudancin Lebanon.

Babban sakataren MDD, Kofi Annan, wanda ke magana daga birnin Rum, yayi kira ga Isra'ila da ta binciki wannan lamari da ya kira "harin da aka auna da gangan" a kan tashar ta sojojin MDD.

Amma kuma wani jami'in diflomasiyya an Isra'ila ya fada wa gidan telebijin na CNN cewar kasar ta yahudawa ba zata taba kai hari da gangan a kan wata tashar MDD ba. A cewarsa, kuskure ne a ce wannan harin da gangan ne, kuma bai ma dace a fadi hakan ba.

Isra'ila ta ce tana takaicin mutuwar sojojin kiyaye zaman lafiyar, kuma zata binciki wannan al'amari.

A halin da ake ciki, shugaban kungiyar Hezbollah, Sheikh Hassan nasrallah, ya ce kungiyarsa za ta fara harba rokoki can cikin Isra'ila, ba wai a kan birnin haifa mai tashar jiragen ruwa a arewacin kasar kawai ba.

A cikin wani jawabinsa da aka nuna a telebijin yau laraba, Sheikh nasrallah ya ce wannan rikicin da suke yi da Isra'ila ya shiga wani sabon babi, babi na kai hare-hare nesa da birnin Haifa.

Hezbollah ta harba rokoki da dama zuwa arewacin Isra'ila tun lokacin da aka fara wannan rikici makonni biyu da suka shige. Isra'ila ta ce watakila kungiyar ta Hezbollah tana da rokoki masu cin dogon zango wadanda zasu iya kaiwa birnin Tel Aviv.

XS
SM
MD
LG