Jami’an Iraq da na Amirka sunce ‘yan gwagwarmaya sun kai hare hare kuma sun kashe ‘yan kasar Iraq 11 da Amirkawa 2. Wani Bam na cikin mota da ya tashi a kasuwa anguwar Sadar na birnin Bagadaza ya kashe akallan mutane 4 a jiya Alhamis sannan fiye da 20 sun ji rauni.
Wani tashin bam din kuma a birnin ya jiwa mutane da dama rauni. A yankin arewacin kasar kuma, wasu mahara sun kai hari a ciki da wajen garin Baquba, sun kashe a kallan mutane 6 kuma an harbi wani sojan Iraq dake gadin waje mai man Fetur, ya mutu.