Ƙungiyar ’yan yaƙin sa kan Nigeria ta Movement for the Emanicipation of the Niger Delta a yankin Niger Delta mai arzikin mai tace an kashe mata mayakan aƙalla guda goma a arangamar da suka yi da sojojin Nigeria.
Ƙungiyar tace a jiya lahadi da dare sojoji suka kaiwa yan ƙungiyar hari a jihar Bayelsa. Ƙungiyar tace an fafata ne a yayinda mayaƙan ke kokarin sako ma’aikacin kamfani mai na Shell da suka sace a kwanan nan. Kamfani mai na Shell ya tabbatar da cewa a ranar takwas ga wannan wata an sace wani ma’aikacinsa a Bayelsa.
Idan ba’a mance ba a makon jiya shugaba Obasanjo ya ce ba zata saɓu ba bindiga a ruwa, lokacinda ya bada sanarwar cewa za’a murkushe yan tawayen bayan da aka yi ta sace ma’aikatan mai. A shekaranjiya asabar rundunr sojan Nigeria tace ta kama fiye da yan yaƙin sa kai ɗari a sumamen da soja suka kai.