Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Firayiminista Nouri Almaliki yace ana samun saukin Tashin hankali a Iraq sai dai...


Firayiministan Iraq, ya ce halin tsaro a kasar Iraq yana kyautatuwa sai dai jiya Lahadi an ci gaba da samun tashi hankali harma mutane 40 sun mutu. Firayiminsta Nouri Al’maliki ya fadawa gidan Talbijin na Cnn jiya lahadi cewa nan gaba kasa da shekara guda sojojin Iran za su iya daukar nauyin ayyukan tsaron kasar ba tare da taimakon sojojin kawance ba. Haka kuma ya ce Iraq ba zata fada yakin basasa ba, kuma baya jin za’ayi. Tunin sojojin kasar Iran sun fara daukar nauyin tsaro a wasu lardunan kasar kuma suna shiri kara karbar ayyukan tsaron wasu lardunan nan da karshen wannan wata.

Mr. Maliki ya yi wannan jawabi na jiya lahadi kwana guda tak bayan da ya janyo ra’ayin shugabannin ‘yan Sunni da ‘yan Shi’a akan su hada kai su yaki masu tada hankali da sunan banbancin jinsin addini a kasar. Jami’an kasar Irq sun bada rahoton cewa an sami wasu ‘yan ci gaba a kasar a wannan wata abinda ya nuna an sami saukin tashe tashen hankula da aka saba samu tun watan janairun bana zuwa watan Yuli wata mafi muni a tashe tashen hankular kasar ta gani tun daga lokacin da sojojin kawance da amirka ta Jagoranta suka mamaye kasar.

XS
SM
MD
LG