Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Jirgin Saman Sojan Nijeriya Ya Fadi Dauke Da Manyan Hafsoshin Sojan Kasar


Hukumomin Nijeriya su na ci gaba da binciken musabbabin hatsarin wani jirgin saman sojan da ya faru jiya lahadi. Wannan jirgin sojan Nijeriya ya fadi jiya lahadi a yankin kudu maso gabashin kasar dauke da manyan hafsoshin soja da dama.

An ce jirgin ya taso ne daga Abuja, babban birnin Nijeriya a kan hanyarsa ta zuwa Obudu a kusa da bakin iyakar kasar da Kamaru.

Yayin da hukumomi a can Nijeriya kuma suke kokarin sanarda iyalan wadanda abin ya shafa, Sashen Hausa na Muryar Amurka ya samu karin haske game da mutanen dake cikin wannan jirgi.

Bayani ya nuna cewa akwai kimanin mutane 17 cikin wannan jirgi da ya fadi a tsakanin jihohin Binuwai da Cross River.

Wata majiya mai tushe ta fadawa Sashen Hausa na Muryar Amurka cewa manyan hafsoshin sojan dake cikin wannan jirgi sune:

  1. Manjo-Janar Nuhu Bamalli (GOC, 2nd Div) Manjo-janar Adeseloyne (GOC, 81 Div) Manjo-janar S. Lemu (Chief of Admin., Army HQ) Manjo-janar Braimoh Manjo-janar Adoga (ana tababar ko yana cikin wannan jirgin ko kuma bai shiga ba) Manjo-janar Agbata Manjo-janar Otubu Manjo-janar Amedo(Commander, Army Corps of Signals) Birgediya-Janar Duniya Birgediya-Janar Haruna Wing Commander Balogun (matukin jirgin) Wing Commander Adekunle (matuki na biyu) Wasu hafsoshi 3 masu mukaman Leftana-kanar da ba a bayyana sunayensu ba Wasu ma'aikatan jirgin su biyu
XS
SM
MD
LG