Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Hukumomi A Kasar Estonia Sun Tsare Jirgin Ruwan Da Ya Jibge Dagwalo A Kasar Cote D'Ivoire


Hukumomi a Estonia sun umurci wani jirgin ruwa mai alaka da abin fallasar dagwalon da aka jibge a kasar Cote D’Ivoire da ya tsaya cikin tashar da yake yanzu, yayin da ake gudanar da binciken aikata mummunan laifi.

Jiya laraba masu gabatar da kararraki na kasar Estonia suka bada sanarwar kaddamar da binciken aikata mummunan laifi, a bayan da gwaje-gwajen kimiyyar da aka gudanar a cikin jirgin suka nuna har yanzu akwai burbushin irin dagwalo mai guba da ya sauke a kasar Cote D’Ivoire. Suka ce jirgin ruwan mai rajistar kasar Panama zai ci gaba da tsayuwa a tashar jiragen ruwan Padilski yayin da ake ci gaba da gudanar da wannan bincike.

Amma kuma kamfanin kasar Netherlands ko Holland da ya mallaki jirgin ruwan ya ce ba wai an kwace shi ba ne, kuma shi ma kansa ya kaddamar da bincike dangane da abin fallasar jibge dagwalon.

A watan da ya shige aka jibge wannan dagwalo ba bisa ka’ida ba a birnin Abidjan. Cote D’Ivoire ta bukaci Estonia da ta tsare jirgin ruwan a bayan da mutum na takwas ya mutu a kasar dake Afirka ta yamma a sanadin gubar dake cikin wannan dagwalo. Wasu dubban mutanen sun kamu da rashin lafiya a bayan da suka shaki tururi mai guba dake tashi daga wannan shara.

XS
SM
MD
LG