Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Rahoton Bayanan Asiri Ya Zamo Batun Yakin Neman Zabe A Nan Amurka


Wani rahoton bayanan asiri na Amurka a kan yakin Iraqi da kuma ta’addanci ya zamo muhimmin batun yakin neman zabe ga ’ya’yan manyan jam’iyyu biyu na nan Amurka ana saura makonni kadan kafin a gudanar da zaben ’yan majalisar dokoki na tsakiyar wa’adin shugaba.

A jiya laraba, ’yan jam’iyyar Democrat sun yi ikirarin cewa rahoton ya nuna cewar yakin Iraqi ya haddasa wutar kin jinin Amurka a kasashen Musulmi, ya kuma kara jefa Amurkawa cikin hatsari.

’Yan Republican suka ce rahoton ya tabbatar da cewa Iraqi ta zamo bakin daga a yaki da ta’addanci kuma ba za a iya watsar da ita sai bayan an murkushe tawayen da ake yi a can.

Gwamnatin shugaba Bush ta bayyana wasu sassan rahoton na asiri a ranar talata. Rahoton ya ce rikicin Iraqi yana renon sabbin shugabanni da mayakan ’yan ta’adda. Amma kuma rahoton ya ce idan har aka ga alamun cewa ’yan Jihadi sun sha kashi a Iraqi, mayaka kalilan ne kawai zasu samu karfin guiwar ci gaba da fada.

XS
SM
MD
LG