Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Jami'an Sufuri A Nijeriya Sun Ce Watakila Kuskuren Matuki Ne Ya Janyo Hatsarin Jirgin Saman ADC


Jami’an sufuri a Nijeriya sun ce watakila kuskuren matuki shine babban abinda ya haddasa hatsarin jirgin saman da ya kashe mutane akalla casa’in da tara jiya lahadi a Nijeriya, cikinsu har da Sultan Muhammadu Maccido.

Darekta-janar na Hukumar Kula da Sararin Samaniyar Nijeriya, Roland Iyayi, ya fadawa Muryar Amurka a yau litinin cewa matukin jirgin, kirar Boeing 737, ya ki bin umurnin da aka ba shi na kada ya tashi a lokacin, a saboda rashin kyawun yanayi. Ya ce wasu jirage biyu dake da niyyar tashi a lokacin sun bi umurnin da aka ba su suka jinkirta tashi.

Hukumomi sun ce akwai mutane 106, fasinjoji da ma’aikata, a cikin wannan jirgi da ya subuto kasa ya kama da wuta jim kadan a bayan tashinsa daga filin jirgin saman Abuja. Masu aikin agaji sun ciro mutane bakwai da suka kuna sosai, amma kuma da ransu, daga cikin garwar wannan jirgi.

Daga cikin wadanda suka rasu har da Sultan na Sakkkwato, Muhammadu Maccido. Shine shugaban majalisar koli ta harkokin addinin Musulunci a Nijeriya, kuma ana daukarsa a zaman shugaban al’ummar Musulmi miliyan saba’in dake Nijeriya.

XS
SM
MD
LG