Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Amurkawa Su Na Shirin Gudanar Da Babban Zabe da Zai Iya Sauya Alkiblar Majalisun Dokoki Da Manufofin Kasa


Jam’iyyun Republican da Democrat a nan Amurka sun mike tsaye domin tabbatar da cewar magoya bayansu sun fito kwansu da kwarkwatarsu a zabubbukan da za a gudanar gobe talata a nan Amurka.

Manyan jam’iyyun biyu na Amurka sun tura dubban ’yan aikin sa kai masu goyon bayan akidojinsu, su na bi gida-gida a jihohin da aka fi yin takarar kujerun majalisar wakilai ta tarayya masu muhimmanci da zasu iya sauya alkiblar majalisar.

Kuri’un neman ra’yoyin jama’a da manyan kafofin labarai suka bayyana jiya lahadi sun nuna cewar da alamun jam’iyyar adawa ta Democrat tana da goyon bayan da zata iya kwace shugabancin majalisar wakilai ta tarayya mai kujeru 435. Amma kuma kuri’un sun nuna cewar jam’iyyar Republican mai rinjaye ta ɗan farfado a cikin makonni biyun da suka shige.

’Yan Democrat zasu bukaci karin kujeru 6 a kan wadanda suke da su yanzu domin kwace majalisar dattijai ta tarayya. Kuri’un neman ra’yoyin jama’a sun nuna cewar akwai kujerun da har yanzu ba a san gwanin da zai hau kansu ba a jihohi kamar Virginia, Missouri, Montana da Rhode Island.

Kuri’un sun nuna cewar har yanzu yakin da ake yi a Iraqi shine babban batun da ya fi dauke hankulan masu jefa kuri’a. ’Yan Democrat sun ce samun nasarar jam’iyyarsu na nufin sauya dabara a kasar Iraqi.

Har yanzu shugaba Bush yana ci gaba da yakin neman zabe wa ’ya’yan jam’iyyarsa ta Republican, kuma a yau litinin ma zai yada zango a jihohi kamar Florida, Arkansas da Texas. A jiya lahadi, ya fadawa magoya baya a Jihar Nebraska dake yammacin kasar nan cewa duniya gaba daya ta dada kyau a saboda shawarar da ya yanke ta cire Saddam Hussein daga kan mulki.

XS
SM
MD
LG