Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Jam'iyar Dimokrat ta lashe kujerun majalisar wakilai


Jam’iyar Dimokrat ta sami nasar lashe Karin kujeru 15 da take bukata ta kwace majalisar wakilai Amirka. A manyan jihohin yankunan gabashi da kudancin ne ta nasarar da zai bada tamar kwace majalisar wakilan Amirka. Kafin a rufe jefa kuri’a a wasu jihoji, jam’iyar ta yi nasarar a jihohi 10 inda ta ture ‘yan majalisar wakilai ‘yan jam’iyar Republican su 10 dake kan kujerun majalisar.

Wasu daga cikin Jihohin sune Indiana, Kentucky and Connecticut. Kwata kwata jam’iyar Demokrat ta sami kujerun majalisar wakilai fiye da 140 daga mazabun kasa baki daya. Su kuma ‘yan jan’iyar Repulican su na da kujerun wakilai 112 ko fiye da haka. Anyi takaran kujerun majalisar wakilai 435 na Amirka baki daya.

A karshen wannan zabe jam’iyar Dimokrat ta lashe zaben kujerun majalisar wakilai kuma jam’iyar za ta nada wata mace mai suna Nancy Pelosi daga jahar California ta zama mace ta farko da zata taba rike mukamin kakakin majalisar wakilai a tarihin Amirka. Tun da fari Nancy pilosi ta ce idan sun sami nasara a majalisar wakilai zasu fito da dokoki masu yawa na gyaran kasa. Tace basu da niyar tsige shugaban kasa, sudai gyara za su yi.

A majalisar dattijai kuma jam'iyar Dimokrat tana neman karin kujeru 3 kafin ta kwace majalisar daga hannun 'yan jam'iyar Republican, ana hasashen cewa kan gari ya waye watakila ta sami nasara.

XS
SM
MD
LG