Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Hukumomin Kasar Chadi sun kafa dokar Ta baci...


Hukumomin Kasar Chadi, sun kafa dokar ta baci, bayan wasu fadace-fadacen kabilanci a gabashin kasar sunyi sanadiyyar rasuwar daruruwan mutane. Yau Litinin aka kafa dokar, wadda ta hade da yankunan Ouaddai, da Salamat,da Wadi Fara, kuma Karin wasu yankuna uku, ciki har da babban birnin kasar, Ndjamena.

Gwamnatin ta Kasar Chadi tace an ta kafa dokar ta bacin ne saboda tsaida tashin hankali da bijirewa doka. A satin da ya wuce dai Hukumar Kula da ‘Yan Gudun Hijira ta Majalisar Dinkin Duniya, ta bayar da sanrwar cewa wasu mahaya dauke da makamai sun kone a kalla kauyuka tara, tare da sace kadarorinsu, a nan kudu maso gabashin Chadin.

Hukumar ta ce tana da bayanan kisar mutane sama da 200 da aka kashe. Mazauna wadannan kauyuka dai sunce Larabawa ne suka kai masu farmakin. Majalisar Dinkin Duniya dai tace tana yiwuwa maharani daga yankin Darfur na Kasar Sudan Suka tsallako cikin Chadin.

XS
SM
MD
LG