Shugaba Bush na Amirka yace kasashen duniya zasu kafawa kasar Iran Takunkumin karya tattalin arziki idan ta ci gaba da inganta sinadaren uranium a matsayin wani bangare na shirin Nukiliyarta mai sarkakakiyar da ake jayayya da ita. A ranar litinin ne Mr. Bush ya yi wannan kalamin a fadarsa ta White House a bayan da ya kare ganawa da firayi ministan Isra’ila Ehud Olmert, Mr. Bush ya ce idan kasar Iran tana da makaman Nukiliya a hannunta, zata iya zama barazana ga zaman lafiya a yankin.
Shugaban na Amirka yaki a zauna ido da ido ya tattauna da shugaban Iran din yana mai cewa Amirka a shirye take tayi magana da iran amma bisa sharadi in ta dakatar da wannan aiki nata, Kamar yada kwamitin sulhu na MDD ya bukaci tayi.
Firayi ministan Isra’ilan yace a yana goyon bayan kokarin Amirka na neman a kafawa kasar Iran Takunkumi. Shi kuwa shugaban kasar partisan Mahmoud Ahmadin Nejad jiya Litinin ya sake nanata barazanar da yayi can kwanaki akan isra’ila cewa yakamata a share kasar daga taswirar duniya baki daya.
Ya ce Isra’ila zata bace nan bada jimawaba. A lokaci da ake hira da shi a gidan Talbijin na NBC Firayiministan Isra’ila ya ce kasarsa ba zata amincewa kasar Iran ta mallaki Nukiliya ba. Sai dai ya ki fadan ko kasarsa zata kaiwa Parisa farmakin ba-zata nan gaba.