Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shugaba Bush Yayi Alkawarin Ci Gaba Da Hada Kai Da Kasashen Asiya


Shugaba Bush ya fara rangadin yankin kudu maso gabashin Asiya tare da yin alkawarin cewa Amurka zata ci gaba da hada kai da yankin domin bunkasa arziki da tsaro a can.

Mr. Bush ya gabatar da jawabi yau alhamis a Jami'ar Kasa ta Singapore. Ya ce muradun Amurka, sun dogara ne a kan abinda ya kira, "fadada 'yancin walwala da dama" a tsawon yankin tekun Pacific.

Ya kuma lashi takobin cewa irin hadin kan da Amurka zata ringa bayarwa a yankin zai kasance na kawance ne ba na yin katsalanda ba.

Singapore ita ce zangon shugaban Bush na farko a rangadin kwanaki takwas da zai yi a kasashe uku a yankin. Daga nan zai zarce zuwa Vietnam domin halartar taron kolin shekara-shekara na Kungiyar Hadin Kan Tattalin Arziki a Yankin Asiya da Tekun Pacific, APEC.

A jawabin da yayi a yau alhamis, Mr. Bush yayi kira ga gwamnatocin kasashen APEC da su taimaka wajen sake farfado da shawarwarin cinikayya a duniya, su kuma nazarci kafa yankin da za a kawar da dukkan shigayen cinikayya cikinsa a fadin gabar tekun Pacific.

Har ila yau ya ce Koriya ta Arewa tana daya daga cikin wadanda suka fi yin barazana ga tsaron yankin. Yayi kira ga shugabannin yankin da su bayyanawa Koriya ta Arewa a fili cewar ba za a kyale ta, ta samar da makaman nukiliya ko makamantansu ga gwamnatocin dake nuna gaba ko kuma ga 'yan ta'adda ba.

Shugaban yayi marhabin da shawarar Koriya ta Arewa ta komawa ga shawarwarin kasashe shida game da shirinta na nukiliya. Amma kuma ya ce tilas ne ta aiwatar da yarjejeniyar da aka cimma a 2005 wadda ta bukaci ta watsar da makamanta na nukiliya domin a ba ta tabbacin tsaro tare da wasu abubuwa na saka mata.

XS
SM
MD
LG