Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Firayiministan Lebanon yace zai ci gaba da zama kan kujerarsa..


Firayi Ministan kasar Lebanon ya ce zai ci gaba da kasance akan mukaminsa duk da ganin zanga-zangar da ‘yan Hezbullah su ka yi na neman ya rusa gwamnatinsa da ke samun goyon bayan kasashen yammaci.

Cikin jawabin da yayi jiya Lahadi, Firyiminista Fuad Siniora ya ce ta hanyar zama a tattauna ne kadai za’a warware wannan rikici. Ya yi kira ga kakakin majalisar Dokokin kasar Nabih Berri da ya sake dago shawarwari da ya cije tsakanin bangarorin kasar dake gaba da juna.

A daidai lokacin da Mr Siniora yake jawabi ne dubban masu zanga-zangar kin jinin gwamnatinsa a karkashin jagorancin ‘yan kungiyar Hezbulla dake samun goyon bayan kasar Syria, suka yi wani gangami a birnin Beiru a rana ta uku a jere.

Masu zanga zangar sun lashi takwabi akan zasu ci gaba da kasancewa akan titunan birnin sai lokacin da Mr Siniora ya sauka daga mukaminsa. Sakataren Janar na kungiyar Tarayar Larabawa Amar Mousa yana birnin Beirut domin tattaunawa da shugabannin kasar a wani kokari na warware wannan rikicin. An kashe wani mutum a wata arangama tsakanin‘yan adawa da kuma masu goyon bayan gwamnati a birnin Beirut .

XS
SM
MD
LG