Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kotun Koli Ta Nijeriya Ta Maida Rasheed Ladoja Kan Kujerar Gwamnan Jihar Oyo


Kotun koli ta Nijeriya ta yanke hukumcin cewa cire gwamna Rasheed Ladoja da aka yi a Jihar Oyo a kudu maso yammacin kasar, haramun ne, kuma ya saba da tsarin mulki.

A yau alhamis a Abuja kotun kolin ta Nijeriya ta maido da Ladoja kan kujerar gwamnan Jihar, kusan shekara guda a bayan da aka tsige shi bisa zargin zarmiya da cin hanci.

An yi imanin cewa shugaba Olusegun Obasanjo shine ya kitsa tsige Rasheed Ladoja da kuma wasu gwamnonin hudu. Amma kuma matakan da aka bi wajen tsige gwamnonin duk sun kaucewa tsari, abinda ya janyo soke-soke masu yawa da zafi.

Wani jami’in kungiyar lauyoyi ta Nijeriya, Lawal Rabana, ya ce wannan hukumci na kotun kolin babbar nasara ce ga dimokuradiyya a Nijeriya.

Wannan hukumcin kuma, yana iya nufin cewa watakila sauran gwamnoni hudu da aka cire daga kan mukamansu cikin ’yan watannin nan su na iya sake komawa kan kujerunsu idanm sun samu nasara a kararrakin da suka shigar.

Masu fashin bakin siyasa sun ce an yi ta tsige-tsigen gwamnonin ne domin karfafa matsayi da muradun shugaba Obasanjo kafin muhimmin zaben da za a yi a shekara mai zuwa.

XS
SM
MD
LG