Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ana Shirin Zartas Da Hukumcin Kisa A Kan Saddam Husein


Lauyoyin Saddam Hussein sun ce Amurka ta mika shi ga hukumomin Iraqi a yayin da ake shirin zartas da hukumcin kisa a kansa.

Amma kuma wani kakakin ma’aikatar harkokin wajen Amurka a nan Washington ya ce har yanzu ba a mika Saddam ga su hukumomin na Iraqi ba. Har ila yau babu tabbas a kan ko yaushe ne za a kashe shi.

Firayim ministan Iraqi, Nouri al-Maliki, ya ce ba za a sake nazari ko jinkirta aiwatar da wannan hukumcin kisa da aka yanke masa ba. Mr. Maliki ya ce duk masu yin adawa da hukumcin kisan da aka yankewa Saddam su na cin zarafin tunanin mutanen da ya gallazawa ne.

Tun fari a yau Jumma’a, lauyoyin Saddam sun ce rundunar sojojin Amurka ta bukace su da su je su kwashe kayan tsohon shugaban.

A ranar talata, wata kotun daukaka kara ta Iraqi ta bayar da umurnin da a zartas da hukumcin kisan cikin kwanaki talatin.

Sojojin Amurka sun kama Saddam a watan Disambar 2003, watanni takwas a bayan farmakin da ya hambarar da shi daga kan mulki. A watan Oktoba wata kotu ta same shi da laifin kashe ’yan mazhabin Shi’a 148 cikin shekarar 1982.

XS
SM
MD
LG