Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ban Ki-Moon Ya Tabbatarwa Da Kwango-Ta-Kinshasa Cewar Ba Za A Janye Sojojin Kiyaye Zaman Lafiya Haka Kwatsam Ba


Babban sakataren Majalisar Dinkin Duniya, Ban Ki-moon, ya tabbatarwa da kasar Kwango-ta-Kinshasa cewar ba za a janye sojojin kiyaye zaman lafiya na majalisar dake kokarin wanzar da kwanciyar hankali a kasar nan kusa ba.

A lokacin da yake magana a Kinshasa, babban birnin kasar, Mr. Ban ya ce za a janye sojojin kiyaye zaman lafiya na Majalisar Dinkin Duniya su kusan dubu ashirin dake kasar ne sannu a kan hankali, kuma za a tattauna yawan wadanda za a ringa janyewa lokaci-lokaci tare da gwamnatin Kwango.

Ya ce tilas ne Kwango ta horar da dakarun tsaronta domin tabbatar da kwanciyar hankali na lokaci mai tsawo, a bayan zaben dimokuradiyyar da aka yi a bara, irinsa na farko a cikin shekaru arba'in da wani abu.

Kungiyar agaji ta Oxfam ta yi kashedin cewa rage sojojin kiyaye zaman lafiya zai haddasa fitina a kasar Kwango-ta-Kinshasa. Kasar tana ci gaba da kokarin tabbatar da wanzuwar zaman lafiya tun bayan karshen yakin basasar shekaru biyar a shekara ta 2002.

XS
SM
MD
LG