Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

VOA ta shirya taron bita akan shirin yaki  da cutar murrar Tsuntsaye


Ita wannan Hukuma, uwa ce ga Muryar Amurka, kuma ta bada tallafi ga ayyukan hana yaduwa cutar murar Tsuntsaye ta hanyar shirya kwasa-kwasai a cibiyoyi 6 a nahiyar Afirka, cikin watan jiya watan Janairu, 2007.

Uku da cikin cibiyoyin bada horon, suna Nigeria, a garuruwan Kano, Abuja da kuma Lagos. Darektan sashen bada horo ga ‘Yan Jaridu na kasa-da-kasa, Joan Mower, wacce ta jagorancin shirin horaswan, tace makasudin gudanar da horon ga “yan Jaridan Nigeria game da cutar Murar Tsuntsaye, shine a kara ilmantar da manema labarai su san meye ita wannan cuta domin sabuwar cuta ce a Duniya bakidaya masanman a Afurka.

Ta ce muddin ana bukatar wayar da kan jama’a a kasashen da cutar Murar Tsuntsaye ta bulla, wajibi ne ‘yan Jaridu su sami cikakken ilimin wannan cuta da sahihiyar hanyar watsa labarai masu sosa rai ga jama’a batare da sun firgita ko damuwa ba. Kwas din, ya hada da dauko tarihin cutar Murar Tsuntsaye, asalinta, yadda take yaduwa tsakanin tsuntsaye.

An kuma bayyana wa mahalarta taron cewa cutar tana iya yaduwa daga tsuntsaye zuwa Alade (alhanzir) ko kuma daga tsuntsaye zuwa Dan Adam – wannan shine mafi muni a ciki domin yana kisa farar-daya kuma ga saurin yaduwa a tsakanin al’uma, muddin dai ba a dauki kwararan matakan hana yaduwar cutar ba.

Abin sha’awa da wannan kwas din, an samu shahararrun Yan jaridu biyu – wato Dan Rutz, tsohon mai bada ruhotannin kan harkokin kiwon lafiya a gidan Talabijin na duniya wato CNN dake Amurka, wanda yanzu yake aiki da Cibiyar binciken cutuka da hana yaduwarsu ta Amurka da shugaban Sashen Hausa na Muryar Amurka, Mr. Sunday Dare. Dukkan su sun gabata da kasidu kan sabbin dabaru da sahihan hanyoyi fadakar da jama game da muggan cutuka masu saurin yaduwa da hanyar kwakulo labarai daga jama’a.

Bangaren Likitoci kula, akwai Shahararren likitan Dabbobi, Dr Shehu Bawa, wanda shine Mukaddashin Darektan hana yaduwar cutar Dabbobi ta Jihar Kano da kuma likitan daya kware a fanin cutuka, duk sun gabatar da lacca kan yadda lamurra suke da hanyoyin samun nasarar yaki da su. A karshen kwas na ko wace cibiya, an jagoranci ‘yan Jaridun da suka halarci taron zuwa kasuwar kaji don yin hira da masu sayar da kaji. Galibin tambayoyin, sun ta’allaka ne akan wuraren da ake sayo su, ko ana bincika lafiyarsu a kasuwar? Shin ko sun san alamomin cutar murar tsuntsaye ? kuma in kaza ta harbu, me yafi dace wa suyi? Manufa a nan shine, su gane cewa cutar murar tsuntsaye tana yaduwa ta hanyar sufuri daga gonar da kaji suka harbu zuwa kasuwa, kenan sayen tsuntsaye da akwagi masu ban-sha’awa daga kasuwa akai gida, na iya yada cutar, muddin dai sun harbu da cutar a kasuwa.

Babban abinda mahalarta taron suka karu da shi, shine sigar yin tambayoyi ga kwararru don samun sahihin amsa, dabarun kwakulo labarai daga mahukunta da maaikatan gwamnati, wadan da basu son hira da manema labarai. Wannan ya kara taimakawa wajan gaggauta fadakar da jama’a game da abinda ka’iya cutar da su. An kuma gargadi ‘yan Jarida, da kada su dauka su kwararru ne don suna da masaniya game da ko wace irin cutuka. Abu na karshe shine dai-daita labarai, ma’ana – a sanar da bullar cuta, inda ta bulla, wadanda ta sha, illarta ga al’uma da kuma matakan da hukuma ta dauka don magance lamarin duk cikin ruhoto guda.

XS
SM
MD
LG