Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

kasar Indonesia taki tabada samfurin H5N1


Gwamnatin kasar Indonesia t ace zata ci gaba da rike samfurin kwayar cutar murrar Tsuntsaye saboda wani sabon shirin hadin guiwa na sarrafa sabon maganin rigakafin cutara tsakaninta da wani kamfanin Amirka. To amma masana ilmin kimiyya na ganin hakan da take son yi na iya jinkirta kokarin da kasashen duniya keyi na sarrafa maganin rigakafin cutar da ake ganin wata kila zai hana yadon cutar daga tsuntsu zuwa dan Adam a duk fadin Duniya.

A wannan makon ne kasar Indonesia ta sanya hannu kan wata takardan yarjejeniya ta fahintar juna da wani kamfanin sarrafa magunguna na Amirka mai suna Baxter International domin yin maganin rigakafin cutar wanda dan Adam zai karba.

To amma tun shekarar da ta wuce tattaunawa tsakanin kamfanin Baxter da kasar Indonesia ya fara kankama, sai gashi kasar ta shiga kin bada samfurin nau’in H5N1 na kwayar cutar mashashsharar tsuntsaye da aka samu a kasarta ga cibiyoyin nazarin cututtukar tsuntsaye na kasashen waje, ko na hukumar lafiya ta duniya. Kasar Indonesia bata fadi dalilinta na hana wasu samun samfurin kwayar cutar ba. To saidai kuma kasar Thailand da wasu kasashe masu tasowa, sun nuna damuwar cewa za’a aike da samfurin wannan kwayar cuta zuwa ga kasashen yammaci domin ayi amfani dashi wajen sarrafa kwayar maganin cutar sannan ‘yan kasashensu da aka samu samfurin daga wajensu ba zasu iya sayan maganin da kudin sub saboda tsada.

Kakakin hukumar Lafiya ta duniya Dick Thompson yace ba dole a batun bada samfurin wannan cuta. Duk kasar da take da samfurinsa anaso ne ta bayar don radin kanta. Kuma har yanzu ba’a gane ko ta yaya wannan yarjejeniyata da ta sanyawa hannu tsakaninta da kamfanin Baxter zai safi binciken samun maganin cutar ba. Don haka yace hukumar lafiya tana matukar goyon bayan ‘yan cin kasar Indonesia ko kuma duk wata kasa da ta kulla yarjejeniya da kamfanin sarrafa magunguna. To amma yace ko da yake yanzu wannan ba shine abin damuwaba, abinda ke akwai shine a fahimci tsarin irin yarjejeniyar da suka kulla tukuna, im ba haka ba hukumar lafiya ta duniya ba zata iya tantance yadda wannan shiri zai shafi kokarin sa ido na ganin bullar cutar a sassan duniya domin samara da magani ba. Su kuma jami’an kamfanin magani na Baxter sun nuna cewa yarjejeniyar tsakaninsu da kasar Indonesia ba bukaci kasar ta hana samfurin kwayar cutar da take da shi ba.

Kasar Indonesia ta ce wata kila nan gaba zata bada samfurin da take dashi. An sami nau’in kwayar cutar mashashshar tsuntsaye ta H5N1 kusan ako ina cikin duniya kuma cutar ta kashe mutnae 166 a cikin ‘yan shekaru 4 da suka wuce. Bullar cutar a kasar Indonesia yayi sanadin mutuwar kusan rabin adadin mace macen da cutar ta janyo a duniya.

XS
SM
MD
LG