Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Biraniya zata janye sojojinta daga Iraq


Prime Ministan Birtaniya Tony Blair, yace kasarsa zata janya dakarunta dubu daya da dari shida a ‘yan watannin nan masu zuwa, za kuma ta mika ragamar tabbatar da tsaron Birnin Basra ga hukumomin Iraqi. A yau laraba Mr. Blair ya shaidawa Majalisar Dokokin Birtaniya cewa kasar zata rage yawan sojojin da take dasu a Iraqi, daga dubu bakwai da dari daya, zuwa dubu biyar da dari biyar.

Prime ministan yace wasu daga cikin dakarun na Birtaniya zasu kasance a Iraqi har zuwa a kalla shekara ta 2008, muddin dai akwai bukatarsu a kasar. Daga nan washington, mai magana da yawun Fadar White House, Gordon Jhondroe yace Shugaba Bush da Mr. Blair sunyi magana ta wayar tarho a jiya Talata, inda suka tattauna batun janya sojojin na Birtaniya. Kakakin na White House yace yana gani wannan janyewa a matsayin wata alama ta nasara, tunda dakarun Birtaniya sun sami nasarar mika al’amuran tsaro hannun hukumomin tsaron Iraqi.

XS
SM
MD
LG